16 Satumba 2025 - 15:43
Source: ABNA24
Iran: A Yaƙin Gaba, Za Mu Yi Amfani Da Makaman Da Ba Makamai Masu Linzami Ba

Birgediya Janar Ahmad Reza Pourdastan, shugaban cibiyar nazarin dabarun sojan Jamhuriyar Musulunci ta Iran: A cikin yiwuwar yakin nan gaba, za mu yi amfani da makaman da va makamai masu linzami ba

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shugaban cibiyar nazarin dabarun sojan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: A cikin kwanaki 12 na kariyar kai mai tsarki, mun fi fuskantar makiya da makamai masu linzami, amma a nan gaba, idan ya zama dole, za mu fuskanci makiya da wasu nau'o'in makaman.

Amir Pourdastan: A cikin yiwuwar yakin nan gaba, za mu yi amfani da makaman da va makamai masu linzami ba

Birgediya Janar Ahmad Reza Pourdastan, shugaban cibiyar nazarin dabarun sojan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana a cikin wata hira da aka yi da shi, yayin da yake ishara da yakin kwanaki 12: Ya kamata al'ummar Iran su sani cewa sojojin kasar Iran sun tsaya tsayin daka wajen yaki da ma'abuta girman kai duk da takunkumin da aka shafe shekaru 46 ana yi da kuma tilasta wa ma'abota girman kan Amurka, Yahudawa da kasashen yamma mika wuya.

Birgediya Janar Pourdastan ya ci gaba da cewa: A cikin kwanaki 12 na kariya mai tsarki jami'an makiya da jami'an siyasa sun daga hannayensu don nuna mika wuya tare da neman tsagaita bude wuta, lamarin da ke nuni da karfi da iko na karfin sojojin Iran.

Shugaban cibiyar nazarin dabarun soji ya ci gaba da yin jawabi ga al'ummar Iran yana mai cewa: Ku tabbatar da cewa idan makiya na son yin wani yunkuri, to za su fuskanci wani martani mai gauni da zai sa suyi nadama.

Ya kara da cewa: A cikin wannan kariya mai alfarma na tsawon kwanaki 12, mun fi fuskantar makiya da makamai masu linzami, amma a nan gaba, idan ya zama dole, za mu yi anfani da wasu makaman, tare da nuna karfin sojojin Imam Khamenei (Dm) da sojojin musulmi ga duniya.

Amir Pourdastan ya kuma yi ishara da rawar da fasaha ke takawa wajen nuna karfin sojojin, yana mai cewa: “Masu fasahar al'adun kasarmu sun shiga fagage daban-daban, da suka hada da fina-finai da kade-kade, kuma an shirya misalai irin su wakar “Elaaj” da Mohsen Chavoshi ya yi, da kuma fina-finai masu karfi na gaskiya, a wannan fanni, sauran masu fasaha kuma za su iya taka rawar gani wajen kara zaburantarwa.

Shugaban cibiyar nazarin dabarun soji ya kammala da cewa: A matsayina na soja, ina kira ga al'ummar Iran da su kasance cikin farin ciki da natsuwa, tare da sanin cewa 'ya'yansu da 'yan uwansu da ke cikin sojojin suna da shirye-shiryen da suka cancanta tare da dacewa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha